4 Disamba 2021 - 14:56
Tattaunawar Vienna, Ta Yi Armashi, Saidai Akwai Jinkiri Daga Kasashen Yamma

Ministan harkokin wajen Iran, ya bayyana tattaunawar Vienna da mai armashi, saidai ya ce akwai alamar jinkiri daga kasashen yamma wajen dagewa Iran takunkumi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA- Hossien Amir Abdolahian, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho jiya Juma’a tare da babban mai kula da harkokin kasashen kungiyar taryyar turai Josep Borrell.

M. Abdolahian Ya ce, kamata ya yi kasashen turai su dukufa wajen cire wa Iran takunkuman Amurka.

Ya kare da cewa duk da sabawar da Amurka ta yi wa yarjejeniyar ba tare da kasashen turan sun dau wani mataki ba, Iran ta koma bakin tattaunawar, da nufin ganin an dage mata takunkuman.

A ranar Litini data gabata ce aka koma bakin tattaunawar a binrin Vienna, bayan tsaiko na watanni biyar sakamakon zuwan sabuwar gwamnati a Iran, saidai a jiya Juma’a bangarorin sun koma gida domin tuntuba game da shawarwarin da Iran ta gabatar masu na neman cire mata takunkunman na Amurka da ta jima tana dangantawa da haramtattu.

342/